fidelitybank

Tinubu ya tafka kuskure zaɓen Musulmi mataimakin – Babachir

Date:

Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayyar Najeriya Babachir Lawal, ya ce, zabin da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Bola Ahgmed Tinubu ya yi na Musulmi a matsayin mataimakinsa gagarumin kuskure ne.

Babachir ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar jiya Talata, inda yake ganin illar hakan kasancewar Tinubun shi ma Musulmi ne.

A ranar Lahadi ne Tinubu ya zabi tsohon gwamnan jihar Borno Kashim Shettima a matsayin mataimakinsa a zaben da za a yi a shekara mai zuwa 2023.

Tsohon Sakataren Gwamnatin wanda ya mara wa Tinubu baya a zaben fitar da gwani na APC, ya ce, zaben na Shettima ya nuna cewa wasu ‘yan baranda kuma ‘yan amshin-shata ne suka takura Tinubun ya yi haka.

Ya ce, bisa ga dukkan alamu, gwamnonin arewa da wasu manyan arewar ne suka sa hakan , da cewa ba za su taba zabar dan takarar da ke da mataimaki Kirista dan arewa ba, kuma shi Tinubun ya yarda da su, in ji Babachir.

Ya yi gargadi da cewa, ”Idan har Tinubun yana ganin wannan zabin shi zai ba shi nasarar samun kuri’un Musulmin arewa, to ya yi kuskure.”

”Saboda za su yi tururuwa su zabi daya daga cikin ‘ya’yansu ne, saboda haka al’adarsu take” In ji shi.

”Buhari, wanda shi ne dansu na fari ba zai kasance dan takara ba a 2023. Amma Atiku dansu na biyu zai kasance.” In ji Babachir.

Saboda haka Tsohon Sakataren yana ganin Atiku Abubakar dan takarar babbar jam’iyyar hammaya, PDP, ‘yan Arewa za su zaba.

sun news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp