Shugaba Bola Tinubu ya tashi daga Abuja zuwa birnin Paris na kasar Faransa a ziyarar ta sirri.
An bayyana hakan ne a wata sanarwa da kakakin Tinubu, Ajuri Ngelale, ya fitar ranar Laraba.
Sanarwar ta ce kawai ziyarar ta sirri ce.
Sanarwar ta kara da cewa shugaban zai dawo kasar ne a makon farko na watan Fabrairu, 2024.
Ku tuna cewa Tinubu ya karbi bakuncin sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken, a ranar Talata.