Shugaba Bola Tinubu ya bar birnin Abuja zuwa Cotonou don halartar bikin cika shekara 63 da kafa Jamhuriyar Benin.
Benin ta samu yancin kai ne daga Faransa a ranar 1 ga watan Agustan 1960, wata biyu kafin Najeriya ta samu nata yancin.
Sanarwar da fadar shugaban ƙasar ta fitar na cewa cikin tawagar shugaba Tinubu akwai gwamnoni guda shida, waɗanda shugaba Patrice Talon ya gayyata da kansa.
Gwamnonin sun haɗa da Dapo Abiodun na jihar Ogun da Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas da Seyi Makinde na Oyo da AbdulRahman AbdulRasaq na Kwara da Nasir Idris na Kebbi da kuma Mohammed Bago na jihar Neja.