Jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Honarabul Dan Asabe Kakanda, ya yi kira ga mai rike da tutar jam’iyyar, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, da ya shiga tsakani ya duba rikicin da ke kunno kai a jihar Adamawa.
Ya ce, rikicin na da nasaba da fitowar Sanata Aishatu Dahiru Binani a matsayin ‘yar takarar gwamna.
Dan Asabe ya bukaci Tinubu da ya bullo da wani tsari na jawo jam’iyyun da za su taru a taron tattaunawa, domin warware duk wata rashin jituwa da ke gabanin zabukan 2023.
A wata sanarwa da Dan Asabe ya fitar, ya bayyana cewa, wasu mutane na hada kai don tayar da rikici suna ikirarin an tafka magudi a cikin atisayen da ya haifar da Sanata Binani a matsayin dan takarar jam’iyyar APC, inda ya nanata cewa, zaben ya kasance daya daga cikin mafi ‘yanci, adalci da kwanciyar hankali da aka taba gudanarwa a jam’iyyar.