Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC mai mulki ya shaidawa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, cewa duk takardun shaidar karatunsa sun bata.
Tsohon gwamnan jihar Legas, wanda ya yi ikirarin cewa, yana da digiri biyu a jami’o’in Amurka guda biyu, ya kara da cewa, “wasu wadanda ba a san ko su wanene ba ne suka sace takardun shaida a shekarun 1990”.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takardar rantsuwa da Tinubu ya mika wa ofishin zaben, a wani bangare na takardun cancantarsa a zaben shugaban kasa na 2023.
Kamar yadda wasu takardu da INEC ta fitar a ranar Juma’a, dan takarar jam’iyyar APC ya yi ikirarin cewa, ya halarci jami’ar Chicago a tsakanin shekarar 1972 zuwa 1976, inda ya samu digiri na biyu a fannin Tattalin Arziki. Ya kuma ce, yana da B.Sc. a cikin Kasuwanci da Gudanarwa a 1979, da kuma takardar shaida a Asusun Jama’a.
Tinubu ya kuma tsallake bayanai dangane da karatunsa na firamare da sakandare.
“Na yi gudun hijira da kaina daga watan Oktoba, 1994 zuwa Oktoba, 1998. Da na dawo na gano cewa, wasu da ba a san ko su wanene ba ne suka wawure dukiyoyina da suka hada da duk wasu takardu da suka shafi cancantata da takaddun shaida na a shafi na uku a sama.
“A gidana ne jami’an tsaro daban-daban suka yi ta bincike, tun daga lokacin da Majalisar Dattawan Tarayyar Najeriya ta tilastawa dakatar da zamanta, bayan da sojoji suka karbe ragamar mulki a ranar 17 ga watan Nuwamba, 1993.