Tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Tinubu, ya sayi fom ɗin jam’iyyar APC a kan kuɗi Naira miliyan 100 na tsayawa takarar shugaban kasa da kuma nuna sha’awa, kamar yadda jaridar PUNCH ta rawaito.
Rahotonni na cewa, Tinubu wanda ya tafi kasar Saudiyya aikin Hajji, ya samu wakilcin wasu makusantan sa da suka hada da dan majalisar wakilai daga mazabar tarayya ta Ikeja, James Faleke; dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Agege a zauren majalisar, Babatunde Adejare; da kuma tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal.
Faleke da Lawal da sauran masu biyayya ga jigo a siyasar Legas ne suka siyo masa fom din takarar shugaban kasa a shelkwatar jam’iyyar APC ta kasa da ke titin Blantyre, Wuse 2, Abuja, da misalin karfe 3 na rana.