Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala ziyarar kwanaki uku a Brazil.
Da misalin karfe 1:20 na daren Laraba ne jirgin shugaban ya isa filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke babban birnin ƙasar Abuja, inda ya sami tarba daga manyan jami’an gwamnati da jagororin siyasa.
Tun da farko Shugaban ya soma ne da zuwa Japan inda ya halarci taron bunkasa yankin Afrika karo na 9 a birnin Tokyo kafin zuwa Brazil.
Ziyarar tasa zuwa ƙasashen biyu na nuna yadda Najeriyar ke ƙoƙarin ƙarfafa alaƙar tattalin arziki da ta diflomasiyya da manyan ƙasashen duniya.
Ziyarar ta kuma mayar da hankali kan yin tattaunawa kan kasuwanci da tsaro da noma da makamashi, da nufin janyo hankalin masu zuba hannun jari.
Shugaban ya shafe kusan makonni biyu a tafiyar ta sa.