fidelitybank

Tinubu ya sauka a Saudiyya gabanin taron ƙasashe Musulmai

Date:

A ranar Lahadi ne shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya isa Riyadh babban birnin kasar Saudiyya domin halartar taron hadin gwiwa tsakanin kasashen Larabawa da Musulunci.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar, Bayo Onanuga ya fitar.

Sanarwar ta ce, Tinubu ya sauka a filin jirgin sama na Sarki Abdulaziz da karfe 10 na safe agogon kasar, kuma mataimakin gwamnan yankin Riyadh, Yarima Mohammed Bin Abdulrahman Bin Abdulaziz ya tarbe shi.

Taron wanda ke gudana bisa gayyatar Sarki Salman da Yarima mai jiran gado Mohammed Bin Salman, zai mayar da hankali ne kan halin da ake ciki a Gabas ta Tsakiya.

Tun da farko Onanuga ya ce taron zai tattauna wasu muhimman batutuwan yankin, musamman kan rikicin Isra’ila da Falasdinu.

A cewar Onanuga, Shugaban Najeriyar zai yi magana kan rikicin, inda ya jaddada matsayar Najeriya na tsagaita bude wuta cikin gaggawa da kuma bukatar gaggauta warware rikicin cikin lumana.

Ya kuma kara da cewa, Tinubu zai kuma matsa kaimi wajen ganin an sabunta yunkurin kasashen duniya na farfado da tsarin kasa biyu a matsayin hanyar da ta dace ta samar da zaman lafiya mai dorewa.

“A yayin taron, ana sa ran shugaba Tinubu zai yi jawabi kan rikicin Isra’ila da Falasdinu, yana mai jaddada kiran da Najeriya ta yi na tsagaita bude wuta cikin gaggawa da kuma bukatar a gaggauta warware rikicin cikin lumana.

“Najeriya kuma za ta ba da shawarar sake sabunta kokarin sake farfado da tsarin kasa biyu a matsayin hanyar samar da zaman lafiya mai dorewa a yankin,” in ji Onanuga.

Za a fara taron ne a ranar Litinin 11 ga Nuwamba, 2024.

assu today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp