Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya isa jihar Ogun domin ziyarar da ya kai wa sarakunan gargajiya a jihar.
Jirgin Tinubu ya sauka a filin wasa na Dipo Dina International Stadium da ke Ijebu-Ode da misalin karfe 10:17 na safe.
Shugaban ya isa Ogun ne tare da shugaban ma’aikatan sa, Femi Gbajabiamila; mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu; da kuma mai ba da shawara na musamman kan ayyuka na musamman, sadarwa da dabaru, Dele Alake.
Gwamna Dapo Abiodun da tsohon Gwamna Segun Osoba da sauran manyan baki ne suka tarbe shi.
Nan take suka tafi taro da Awujale na Ijebuland, Oba Sikiru Adetona, da sauransu.
Daga nan kuma Tinubu zai koma Abeokuta domin ganawa da Alake na Egbaland, Oba Adedotun Gbadebo a fadarsa ta Ake.