Zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya sauka a Abuja, bayan wata ziyara da ya kai ƙasar Faransa, inda ya shafe tsawon mako biyar.
Tinubu ya sauka ne da yammacin Litinin a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe, da ke Abuja.
Wani bidiyo da ya wallafa ya nuna manyan jiga-jigai da makusantan zaɓaɓɓen shugaban ƙasa ciki har da zaɓaɓɓen mataimakin shugaban, Kashim Shettima da Simon Lalong, babban daraktan rusasshen kwamitin yaƙin neman zaɓen Bola Ahmed Tinubu na dakon saukar sa a filin jirgin sama.
Haka zalika, an ga cincirindon ‘ya’yan jam’iyya mai mulki da magoya bayan Tinubu a lokacin da suka tarbe shi bayan ya sauka da yammacin Litinin.
An yi ta raɗe-raɗi da yaɗa jita-jita game da tafiyar tasa zuwa Paris, inda wasu suka riƙa cewa ganin likita ya tafi, saboda taɓarɓarewar lafiyarsa.
Komawarsa gida Najeriya ta kawo ƙarshen duk irin waɗannan raɗe-raɗi da jita-jita.
Kuma a yanzu saura kwana 35 a rantsar da Bola Ahmed Tinubu matsayin shugaban ƙasa, inda zai karɓi ragamar mulki ranar 29 ga watan Mayu.


