Shugaban kasa, Bola Tinubu, ya daidaita rikicin siyasar jihar Ondo da aka kwashe watanni ana gudanarwa tsanakin bangaren gwamnan jihar Rotimi Akeredolu da mataimakin gwamnan Lucky Aiyedatiwa.
Cikin wata sanarwar da mai magana da yawun shugaba Tinubun, Ajuri Ngelale, ya fitar ranar Asabar, ya ce an cimma hakan ne bayan kwashe lokaci mai tsawo ana tattaunawa tsakanin bangarorin biyu da da ‘yan majalisar jihar da bangaren jam’iyyar APC na jihar kuma shugaban kasar ranar Juma’a a fadarsa da ke Abuja.
Sanarwar ta ce shugaba Tinubu ya shawarci duka bangarorin da su manta da duka abubuwan da suka faru, domin zaman lafiyar jihar da gudanar da ayyukan ci gaba.

Sasancin ya tabbatar da cewa Akeredolu zai ci gaba da zama a matsayin gwamna, yayin Aiyedatiwa zai ci gaba da kasancewa a matsayin mataimaki.
A baya-bayan nan dai an samu rashin jituwa tsakanin majalisar dokokin jihar da mataimakin gwamnan bayan da majalisar ta zarge shi aikata wasu laifuka ciki har da rashin biyayya ga gwamnan jihar.
Lamarin da ya kai har da barazanar tsigewa, inda ya garzaya wata babbar kotu a Abuja wadda ta dakatar da ‘yan majalisar daga yunkurin.