Dokar Kare bayanai ta Najeriya, na shekarar 2023 ta samar da tsarin doka don kare bayanan sirri da kuma aikin kare bayanan a Najeriya.
Dokta Vincent Olatunji, Kwamishinan Hukumar Kare Bayanai ta Najeriya (NDPB) ne ya bayyana haka a taron tabbatar da tsarin NDPD Strategic Roadmap and Action Plan (SRAP) a Abuja, inji rahoton NAN.
An aika da kudirin dokar zuwa majalisar dattawa da ta wakilai domin tantancewa da kuma amincewa da shi a ranar Talata 4 ga Afrilu 2023, ta hanyar wasikar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.
“Yanzu doka ce sabuwar doka ta kafa hukumar kare bayanan Najeriya ta maye gurbin NDPB da tsohon shugaban kasa Buhari ya kafa a watan Fabrairun 2022,” inji shi.
Kwamishina na kasa ne zai jagoranci hukumar da alhakin sarrafa bayanan sirri.


