fidelitybank

Tinubu ya san jam’iyyar da na ke goyon baya – Sanusi

Date:

Yayin da zaben 2023 ke kara karatowa, tsohon Sarkin Kano, Sanusi Lamido Sanusi, ya bayyana jam’iyya daya tilo da ya ke goyon baya.

Sanusi ya ce jam’iyyar All Progressives Congress, APC, dan takarar shugaban kasa, Bola Tinubu na sane da cewa shi na jam’iyyar da ake kira Najeriya ne.

Ya bayyana hakan ne yayin da ya ke cewa shi ba dan kowace jam’iyya ba ne.

Sanusi ya yi wannan jawabi ne a lokacin da yake zantawa da Tinubu da sauran baki a Kaduna a yayin bikin KadInvest karo na bakwai, wanda hukumar bunkasa zuba jari ta jihar Kaduna ta shirya a jiya.

Tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya CBN ya kuma koka da yadda ake satar mai, da karuwar basussukan da Najeriya ke fama da ita, rashin daidaiton biyan tallafin da ake samu da kuma hauhawar kudaden kasashen waje, da dai sauran kalubalen kudi da tattalin arziki da Najeriya ke fuskanta a halin yanzu.

Ya yi kira da a yi gaskiya da rikon amana wajen tafiyar da dukiyar kasa sannan kuma ya bukaci a kwancewa kamfanin man fetur na kasa (NNPC) Limited, yana mai cewa kamfanin ba saniya ba ce amma ya kamata a gudanar da shi a matsayin kamfani mai zaman kansa tare da bin diddigin al’amura.

Sanusi ya kuma bukaci Jihohin kasar da su ‘yantar da kansu daga dogaro da gwamnatin tarayya fiye da kima.

“Na ci gaba da maimaitawa, da fatan ku tuna cewa na rasa aiki a babban bankin kasa saboda wannan matsala.

“Ba batun wata jam’iyya ba ce. Bani da party. Jam’iyyata Najeriya ce. Wannan ita ce matsalar da muka samu a 2014. Asiwaju (Tinubu) ya san jam’iyyata ita ce Najeriya,” inji shi.

www.najnew

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnan Kano ya kori mataimansa na musamman kan belin Danwawu

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da...

Tsohon Minista a mulkin Buhari ya mutu

Allah ya yi wa tsohon ministan noma da raya...

Kashi 70 na yankin Bukuyum ta Kudu na ƙarƙashin ƴan Bindiga – Ɗan majalisa

Rahotanni daga yakin ƙaramar hukummar Bukuyum na jihar Zamfara...

Goodluck ya fi dacewa ya zama dan takara a 2027 – Lamido

Tsohon Gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido ya ce Tsohon...

An gargadi al’umma su yi taka tsan-tsan da ambaliyar ruwan sama

Yayin da ake ci gaba da fuskantar saukar ruwan...

Gwamnatin Tarayya za ta gina hanyar sufurin jirgin ƙasa a Kano

Gwamnatin Tarayya ta ce, za ta samar da titin...

Abin da ya sa muke ci gaba da tsare Sowore – Ƴansanda

Kwamishinan ƴansanda mai kula da sashen kai ɗauki na...

INEC za ta bai wa ɗaurarru damar kaɗa ƙuri’a a lokacin zaɓuka

Hukumar zaɓen Najeriya, INEC ta ta duba yiwuwar bai...

Mai ya jawo Matan Zamfara su ka yi zanga-zanga

Ɗaruruwan mata ne tsofaffi da masu shawarya suka gudanar...

Aƙalla mutane 24,000 ne suka ɓata saboda Boko Haram a Najeriya

Kungiyar Agaji ta Red Cross ta bayyana cewa aƙalla...

‘Yansanda ku gaggauta sakin Sowore – Obi

Tsohon ɗan takarar shugaban kasa a jam'iyyar LP, Peter...

PDP ta gargaɗi mambobinta kan goyon bayan Tinubu

Babbar jam'iyyar hamayya ta PDP a Najeriya ta gargaɗi...
X whatsapp