Kotun koli ta yi watsi da daukaka karar da Peter Obi na jamâiyyar Labour Party (LP) ya shigar bisa dalilansa na rashin cancantarsa.
A hukuncin daya yanke, kwamitin mutane bakwai na kotun ya tabbatar da hukuncin kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa (PEPC) tare da tabbatar da zaben shugaban kasa Bola Tinubu.
Hukuncin da mai shariâa John Okoro ya yanke, wanda bai wuce mintuna biyar ba, ya ce akasarin batutuwan da ke cikin karar Obi sun warware ne a hukuncin da Atiku na PDP ya shigar a baya.
Mai shariâa Okoro ya ce batu daya tilo da ke cikin karar Obi wanda ba a cikin karar Atiku ba shi ne batun nadin mataimakin shugaban kasa Kashim Shettma.
Ya ce tun farko kotun koli ta warware batun da ya shafi Shettima na neman takara sau biyu a hukuncin da ta yanke ranar 9 ga watan Mayu a karar da PDP ta daukaka kan INEC da wasu mutane uku.
Mai shariâa Okoro ya ce bai kamata a sake gabatar da batun a gaban kotun koli ba daga wadanda suka shigar da kara wadanda tuni suka san hukuncin.
Haka kuma kotun ta yi fatali da Ĉarar Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP.


