A halin yanzu dai shugaba Bola Tinubu yana ganawa da tsohon gwamnan jihar, Nyesom Wike da Nasir El-Rufai a fadar shugaban kasa ta Aso Rock Villa, Abuja, inji rahoton Daily Trust.
A cewar jaridar, Wike ya isa gidan gwamnatin ne da misalin karfe 1:40 na rana, yayin da El-Rufai ya shiga bangaren shugaban kasa na Aso Rock da misalin karfe 2 na rana.
Wike da El-Rufa’i sune wadanda Tinubu ya zaba a matsayin ministoci.
Yayin da Majalisar Dattawa ta tantance Wike kuma ta tabbatar da shi, El-Rufai har yanzu ba a wanke shi ba kan wani rahoton tsaro da ake jira.
Akwai rade-radin cewa ana kokarin ganin majalisar dattawa ta tabbatar da Malam El-Rufai.