Shugaba Bola Tinubu ,ya yi kira da a samar da haɗin kai tsakanin gwamnatin tarayya, gwamnonin jihohi da kuma ƴan majalisar tarayya don kawowa Najeriya ci gaba.
Shugaban ya yi wannan kira ne lokacin da ya karɓi bakuncin gwamnonin jihohi da kuma shugabancin majalisar tarayya a gidansa da ke Legas ranar Juma’a.
Tawagar wadda ta samu jagorancin mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima, ta kunshi shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio, shugaban majalisar wakilai Tajudeen Abbas, gwamna AbdulRahman AbdulRazaq na jihar Kwara wanda shi ne shugaban ƙungiyar gwamnonin Najeriya da sauransu.
Da yake magana a madadin shugaban ƙasar, Shettima ya yi fata kan farfaɗowar tattalin arzikin Najeriya, inda ya yi kira ga haɗin kan kowa domin kai ƙasar gaba.
Ya buƙaci haɗin tsakanin dukkan masu ruwa da tsaki tare da yin alkawarin makoma mai kyau ga ƙasar karkashin jagorancin shugaba Tinubu.