Shugaba Bola Tinubu, ya rantsar da mai shari’a Kudirat Kekere-Ekun a matsayin mace ta 23 kuma ta biyu a matsayin shugabar Alkalan Najeriya, CJN a matsayin mukaddashi har sai majalisar dattawa ta tabbatar da hakan.
Ta karbi mukamin ne daga hannun mai shari’a Olukayode Ariwoola, wanda ya yi ritaya a ranar 22 ga watan Agusta yana da shekaru 70 a duniya.