Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu, ya nada karamin ministan kwadago da samar da ayyuka Festus Keyamo, a matsayin babban mai magana da yawun yakin neman zaben sa na shugaban kasa.
Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a fadar shugaban kasa a ranar Alhamis.
Adamu wanda tun da farko ya gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa da ke Abuja, ya kuma bayyana cewa, an nada wata yar jarida Hannatu Musawa a matsayin mataimakiyar kakakin.
A halin da ake ciki, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP kuma tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar ya amince da nadin Dino Melaye da kuma Dr. Daniel Bwala a matsayin kakakin.


