Shugaba Bola Tinubu ya amince da nadin sabbin Daraktoci na Hukumar Leken Asiri ta Kasa, NIA, da Ma’aikatar Tsaro ta Kasa, DSS.
An nada Ambasada Mohammed Mohammed a matsayin sabon Darakta-Janar na NIA yayin da Adeola Oluwatosin Ajayi shi ne sabon Darakta-Janar na DSS.
Hakan ya fito ne a wata sanarwa da mai magana da yawun Tinubu, Ajuri Ngelale ya fitar.
Sanarwar ta ce: “Ambassador Mohammed ya yi fice a hidimar kasar waje tun lokacin da ya shiga NIA a shekarar 1995. Ya yi ayyuka daban-daban, har ya kai ga kara masa girma zuwa mukamin Darakta da kuma nadin sa a matsayin shugaban hukumar ta Najeriya zuwa Libya.
“Wanda ya gama karatu a Jami’ar Bayero Kano a shekarar 1990, ya yi aiki a kasashen Koriya ta Arewa da Pakistan da Sudan da kuma a fadar gwamnati da ke Abuja.
“Sabon Darakta-Janar na DSS, Mista Adeola Ajayi, ya kai matsayin mataimakin darakta Janar na Hukumar. Ya yi aiki a lokuta daban-daban a matsayin Darakta na Jiha a Bauchi, Enugu, Bayelsa, Ribas, da Kogi.
“Sabbin nadin ya biyo bayan murabus din da shugabannin NIA da DSS suka yi a baya.
“Shugaba Tinubu yana sa ran sabbin shugabannin tsaro za su yi aiki tukuru don sake canza hukumomin leken asirin guda biyu don samun sakamako mai kyau tare da tuhume su da su kawo kwarewarsu wajen tinkarar kalubalen tsaro da ke addabar kasar nan ta hanyar inganta hadin gwiwa da hukumomin ‘yan uwa da kuma yin aiki tare da jami’an tsaro. Ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (ONSA).
“Shugaban ya gode wa Daraktocin manyan hukumomin leken asirin guda biyu masu barin gado bisa ayyukan da suke yi wa kasa tare da yi musu fatan samun nasara a ayyukansu na gaba.”