Jagoran jam’iyyar APC kuma mai neman takarar shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya nada, Kwamared Muhammad Mahmud a matsayin shugaban yada labaransa na kasa.
Mahmud mai shekaru 31, dan asalin Jihar Borno, ya tabbatar wa da manema labarai a Maiduguri cewa, suna iyakar kokarin ganin sun tattaro jama’a, kwansu da kwarkwata wurin ganin burin Tinubu ya cika na maye gurbin Buhari a 2023.
A cewarsa,”Nadin nasa bai ba shi mamaki ba, domin salon mulkin Tinubu na daban ne,ina matukar farin ciki kuma zai tabbatar kwalliya ta biya kudin sabulu da yardar Ubangiji”. In ji Kwamrade Mahmud.
Magoya bayan Tinubu sun fito tun a baya, sun baiwa mataimakin shugaban kasa Yemi Osibanjo shawara cewa, da ya janye takarar shugaban kasa da ya ke yunkurin fitowa a jam’iyar APC.