Tsohon gwamnan Legas kuma dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC mai mulki, Asiwaju Bola Tinubu yana kasar Ingila tare da mukarrabansa.
A matsayin wani bangare na shirye-shiryen zaben 2023, ana sa ran Tinubu zai yi jawabi a Chatham House, Landan, kan ‘Renewed Hope Agenda’ a ranar Litinin (yau).
Dan takarar na jam’iyyar APC zai yi karin haske kan tsare-tsarensa na tsaro, tattalin arziki da kuma manufofin kasashen waje a cibiyar nazarin harkokin ketare da manufofinta na Burtaniya nan da ‘yan sa’o’i masu zuwa.
Ya samu rakiyar kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, gwamnonin jihohin Jigawa da Kaduna, Abubakar Badaru, Nasir El-Rufai da kuma tsohon gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi.
Asiwaju ya bayyana a cikin takardarsa na nuni da aniyar kafa wata kyakkyawar manufa da za ta iya samar da ingantaccen tsarin gine-gine don magance ta’addanci da fashi da makami da garkuwa da mutane da sauran nau’o’in miyagun ayyuka da ke haddasa barna a kasar nan.