Tsohon gwamnan jihar Enugu, Sanata Chimaroke Nnamani, ya yaba da yadda dan takarar shugaban kasa na jamâiyyar All Progressives Congress (APC) Asiwaju Bola Ahmed Tinubu yake yi.
Sanatan na Gabashin Enugu ya c,e tsohon Gwamnan Legas ya inganta harkar lafiya sosai.
Nnamani, a cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja, ya ce abun yabo ne ga Tinubu cewa cutar kanjamau ta ragu a jihar Legas daga kashi 6.7 zuwa kashi 3.5 tsakanin shekarar 1999 zuwa 2007 yayin da mata sama da 2,000 suka samu rigakafin kamuwa da cutar kanjamau daga uwa zuwa yara (PMTCT). a cibiyoyi 10 na PMTCT da aka kafa domin rigakafin cutar.
Ya tuna cewa Tinubu ya kaddamar da shirin yaki da cutar zazzabin cizon sauro inda sama da majiyyata miliyan 3.6 suka samu magani kyauta da kuma gidajen sauro sama da miliyan daya da kuma BCC/IEC da aka ba su.
Nnamani ya kara da cewa an samar da allurai sama da 181,627 na sinadarin Sulfadoxine-pyrimethamine, kuma an aiwatar da maganin rigakafin zazzabin cizon sauro na wucin gadi ga mata masu juna biyu.
“Don kawo karshen cutar shan inna, an kaddamar da shirin rigakafi na kasa, jihar Legas ta kasance mai mahimmanci kuma fiye da yara miliyan 2.5 sun karbi maganin,” in ji shi.
A karkashin gwamnatin Tinubu, ya ce, âJihar Legas ta kaddamar da shirin kula da lafiya a makarantu, wanda ya samar da aikin tantance ido da kuma kula da lafiyar dalibai kusan 6,600 da kuma samar da madara kyauta ga makarantun gwamnati sama da 900 da adadinsu ya kai 297,000.
âShirin Kiwon Lafiya da Haihuwa Kyauta na Tinubu, ya kara da cewa, ya shafi yara âyan kasa da shekaru 12 da manya sama da 60 kuma ba tare da tsadar kulawar haihuwa ga mata masu ciki ba.