Gabanin zaben fidda gwani na shugaban kasa da babban taron jam’iyyar All Progressives Congress na kasa, gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni da takwaransa na jihar Borno, Babagana Umara Zulum, sun ce kwazon sa na kasuwanci da siyasa na Asiwaju Bola Tinubu za su fifita shi a sama da sauran ‘yan takara.
Gwamnonin biyu sun bayyana haka ne a lokacin da Tinubu ya ziyarci jihohinsu, domin ganawa da wakilan jam’iyyar a babban taron kasa na fidda da ake shirin gudanar cikin ‘yan kwanaki a Abuja.
Buni ya ce “Tarihin gwagwarmayar dimokuradiyya a Najeriya ba zai iya cika ba sai an ambaci gagarumin ayyukanku, tun daga zamanin NADECO har zuwa yanzu mutum na karshe da ya tsaya ya hana al’ummarmu zama kasa mai jam’iyya daya. Mu a Yobe, wannan gida ne. Kuna nan don tattaunawa da ƴan’uwanku wakilan mu. Yobe ita ce gidanku kuma kuna gida.”
Da yake jawabi a Yobe, Asiwaju Tinubu ya jaddada rawar da jihar ke takawa a juyin juya halin noma a Najeriya. In ji Naija News.