Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) reshen kasar Burtaniya ta bayyana cewa, Asiwaju Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar, yana da kyakyawar lafiya sabanin rade-radin da ake yadawa a shafukan sada zumunta.
Mista Joseph Adebola, shugaban kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC na kasar Birtaniya (PCC) ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis a Abuja.
Ya bayyana rade-radin da ake cewa Tinubu ba shi da lafiya ya tafi kasar waje neman lafiya da cewa ba gaskiya ba ne.
“Abin takaici a gare su, mugun tunanin da suke yi wa Tinubu ba zai tabbata ba, domin su ba Allah ba ne, mai ba da rai.
“Domin bayani, Tinubu ya kasance yana ganawa da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a nan Burtaniya kuma ya ci gaba da kasancewa mai kwazo da kwarin gwiwa.
“A daya daga cikin abubuwan da aka yi kwanan nan a Landan, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Tinubu ya yi wata ganawa mai mahimmanci tare da wasu mambobin tawagar shirin yakin neman zabensa.
“Tawagar ta hada da Alhaji Ibrahim Masari, Sen. Tokunbo Afikuyomi, mataimakin daraktan kwamitin tsare-tsare na PCC, Cif Pius Akinyelure da jiga-jigan ‘yan siyasa masu son ci gaba a nan Burtaniya,” in ji Adebola.
Ya ce an kira taron ne da farko domin yanke hukunci kan wasu batutuwan da suka dade suna tafe, gabanin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC.
Ya kara da cewa, an kammala taron ne da daukar hotuna a wurin taron, wanda a halin yanzu yake ta yawo a shafukan sada zumunta.
“Daya daga cikin hotunan da aka dauka a kafafen sada zumunta ya nuna Asiwaju da tawagarsa suna komawa gida daga lambun.
“Majalisar ta kara tabbatar da halin da Asiwaju Bola Tinubu ke ciki da ayyukan yau da kullum.
“Duk da haka, ba za mu shagala da farfaganda mara kyau ga Asiwaju da jam’iyyar APC ba, yayin da muka kuduri aniyar ci gaba, mu yi imani da Allah da kuma ‘yan Najeriya masu zabe don hawan kujerar shugabancin Tinubu a 2023,” in ji Adebola.
Ya shawarci masu yi wa kasa hidima da su shagaltu da wasu sana’o’in samun riba domin amfanin su.