Tsohon ɗan majalisar wakilai daga jihar Jigawa, Faruk Adamu Aliyu ya ce shugaban kasa,Bola Ahmed Tinubu, yana cikin ƙoshin lafiya ba kamar yadda wasu ke yaɗawa ba.
Hon Faruk ya ce ya yi hannu da shugaba Tinubu a ranar Talata da daddare.
“An yi min waya daga fadar shugaban ƙasa kuma na je kuma mun gana da shi fiye da minti 30, kuma a yadda na gan shi babu alamar ciwo a jikinsa, mun gaisa , mun yi wasa da dariya kamar yadda muka saba sannan mun yi hoto, sai dai kawai alamun dattijantaka,” in ji Faruk Adamu Aliyu.