Shugaban kasaa, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da naɗin ACM Mohammed Shehu, a matsayin sabon shugaban hukumar kiyaye aukuwar haɗurra ta ƙasa.
A cikin wata sanarwa da ta fito daga ofishin sakataren gwamnantin tarayya, Sanata Gorge Akume, sanatwar ta ce, shugaban ƙasa ya amince da naɗinsa bisa tanadin dokar hukumar.
Da farko ACM Shehu zai yi wa’adin shekara huɗu, farawa daga ranar 20 ga watan Mayun 2024, kamar yadda dokokin da suka kafa hukumar suka tanadar.
Shugaba Tinubu ya kuma hori sabon shugaban hukumar FRSC, da ya yi amfani da ƙwarewar da yake da ita, wajen kawo gagarumin ci gaba a sabon muƙamin nasa.
ACM Shehu ya maye gurbin CM Dauda Biu, wanda wa’adin shugabancinsa ya ƙare.