Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da nadin Mista Shaakaa Chira a matsayin babban mai binciken kudi na tarayya, kamar yadda hukumar kula da ma’aikatan gwamnatin tarayya (FCSC) ta ba da shawarar.
A wata sanarwa da Ajuri Ngelale ya fitar a ranar Juma’a, ta ce shugaban kasar ya amince da nadin Chira ne bayan da hukumar da’ar ma’aikata ta kasa (FCSC) ta gudanar da aikin tantance shi a matsayin wanda ya fi cancantar wanda kuma ya samu nasara a jarabawar a tsakanin dukkan wadanda suka cancanci shiga jarabawar ofis.
Ya ce shugaban na sa ran sabon Odita Janar din zai tabbatar da amincewar da aka yi masa tare da cika babban tsammanin da ‘yan Najeriya ke yi dangane da aiwatar da ajandar sabunta fata na gwamnatinsa.
Ya kuma bayyana cewa shugaban kasar ya yi amfani da karfin ikon sa ne da sashe na 86 na kundin tsarin mulkin 1999 ya ba shi kamar yadda aka yi wa kwaskwarima.


