Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya nada babban mai shigar da kara na hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC, Rotimi Oyedepo da wasu shida a matsayin sabbin mataimaka.
An tura sabbin wadanda aka nada zuwa ma’aikatar shari’a ta tarayya da ke Abuja.
Ana nufin su yi aiki a karkashin Babban Lauyan Tarayya (AGF) da Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi.
Sabbin wadanda aka nada sun hada da:
1. Kamarudeen Ogundele, mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin sadarwa da yada labarai
2. Hussein Oloyede, Mataimaki na Musamman akan Tattaunawa, Zayyana da Dokoki
3. Rotimi Oyedepo (SAN), mataimaki na musamman kan laifukan almundahana da bin doka da oda.
3. Monsurat Gafar, mataimakiya ta musamman kan hadin kai da hulda da hukumomin gwamnati.
4. Marcus-Obiene Fernández, Mataimaki na Musamman kan Gyaran Sashin Shari’a da Fasahar sadarwa ta zamani da ƙirƙira.
5. Ahmed Wada, mataimaki na musamman akan ayyuka na musamman.
6. Tolu Obamuroh, mai ba da shawara kan fasaha kan harkokin mai da iskar gas, sasantawa da takaddamar kasa da kasa.