Shugaban kasa Bola Tinubu aike da sunayen shugabannin majalisar gudanarwar sabuwar hukumar raya yankin arewa maso yammacin ƙasa zuwa ga majalisar dattawan ƙasar domin amince wa naɗinsu.
Cikin wata sanarwa da kakakin shugaban ƙasar, Bayo Onanuga ya fitar ya ce matakin na zuwa ne bayan sanya hannu kan dokar da ta amince da ƙirƙiro sabuwar hukumar.
A ranar 24 ga watan Yuli ne dai Shugaba Tinubu ya sanya hannu kan sabuwar dokar.
Mutanen da Shugaba Tinubun ya aike da sunayensu don jagorantar sabuwar hukumar sun haɗa da:
Ambassada Haruna Ginsau (Jigawa) a matsayin shugaban majalisar gudanarwar hukumar.
Farfesa Abdullahi Shehu Ma’aji (Kano) a matsayin shugaban hukumar.
Sauran mambobin hukumar sun haɗa da :
- Dakta Yahaya Umar Namahe (Sokoto)
- Hon. Aminu Suleiman (Kebbi)
- Sen. Tijani Yahaya Kaura (Zamfara)
- Hon. Abdulkadir S. Usman (Kaduna)
- Hon. Engr. Muhammad Ali Wudil (Kano)
- Shamsu Sule (Katsina)
- Nasidi Ali (Jigawa)
Sanarwar ta ci gaba da cewa ana sa ran sabbin shugabannin za su yi amfani da ƙwarewarsu wajen gina sabuwar hukumar.


