Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Tinubu, ya musanta cewa ya yi gaggawar ficewa daga fagen filin yakin neman zabensa a garin Minna na jihar Neja.
Tinubu ya bayyana cewa, jama’ar da suka tarbe shi sun yi yawa har sai da ya yi musu jawabi a takaice kafin ya halarci wasu taruka a jihar.
Dan takarar jam’iyyar APC ya yi watsi da jita-jitar da ake yadawa cewa ya yi gaggawar ficewa daga fagen yakin neman zabe saboda yanayin lafiyarsa.
Ya ce jama’ar da suka taru a wurin taron ba a taba yin irinsa ba.
Ya bayyana hakan ne ta bakin kakakin kungiyar yakin neman zaben sa, Bayo Onanuga.
A wata sanarwa da Onanuga ya fitar na cewa: “Daga cikin dimbin magoya bayan jam’iyyar APC ne suka tarbi dan takarar shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, zuwa Minna a ranar Laraba, a lokacin da ya isa babban gangamin.
“Jama’ar da suka yi ta murna ba a taba ganin irinta ba, kamar yadda ‘yan jarida a harabar baje kolin kasuwanci, inda aka gudanar da taron.
“Tinubu, wanda ya sake gudanar da wani taro mai nasara a Kaduna a ranar Talata, ya isa Minna da yammacin ranar domin ganawa da shugabannin APC.”
Kwanan nan, wasu masu ruwa da tsaki na siyasa sun yi ta kokwanton halin lafiyar Tinubu, cewar ba zai iya jagorantar Najeriya ba.