Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Tinubu, ya taya Archbishop Daniel Okoh na Cocin Christ Holy Church (Odozi-Obodo), murnar zabensa da aka yi a matsayin shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN).
Sakon taya murna na Tinubu na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ofishin yada labaransa ya fitar mai dauke da sa hannun Tunde Rahman.
A ranar Alhamis ne kungiyar CAN ta tabbatar da zaben Okoh a matsayin sabon shugabanta.
Tinubu, wanda ya bayyana cewa, Okoh shine wanda ya cancanta a maye gurbin Ayokunle, ya kuma koka kan yanayin tsaro a kasar nan, yana mai cewa Najeriya na cikin wani mawuyacin hali inda bata gari da munanan mutane ke kokarin ruguza zamantakewar jama’a da kuma haifar da tashin hankali ga kowa.