Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya miƙa ta’aziyyar mutuwar Shugaban Iran Ebrahim Raisi da Ministan Harkokin Waje Hossein Amir-Abdollahian, da sauran abokan tafiyarsu sakamakon hatsarin jirgin sama.
Wata sanarwa daga fadar shugaban kasa ta fitar a Abuja, ta ce, Tinubu ya bayyana damuwa game da hatsarin, kuma ya siffanta Raisi a matsayin shugaban da ya mayar da hankali wajen cigaban Iran.
Da yake taya iyalansa alhini, Shugaba Tinubu, ya yi addu’ar ɗorewar zaman lafiya, da kwanciyar hankali, da kuma cigaban ƙasar Iran.