Shugaban kasa, Bola Tinubu, ya miƙa saƙon ta’aziyyarsa bisa rasuwar mai ɗakin cif MKO Abiola, Dr Doyinsola Hamidat Abiola wadda ƴar jarida ce da ta yi fice.
Sanarwar da aka fitar daga Fadar Shugaban na Najeriya ta ambato irin gudummawar da Doyin Abiola wadda ta rasu tana da shekara 82 ta bayar a fannoni da dama musamman a ɓangaren jarida da kuma samar da daidaito tsakanin jinsi.
Sanarwar ta kuma yi magana kan rawar da ta taka wajen raya dimokraɗiyya inda ta yi riƙo da gaskiya da kuma ƙoƙarin samar da shugabanci na gari.
A cewar sanarwar, shugaban ya bayyana kyakkyawar alaƙar da ke tsakaninsa da marigayiyar wadda ta samo asali daga irin dangantaka ta ƙut da ƙut da ke tsakaninsa da marigayi MKO Abiola.
Ya ce ta bayar da gudummawa a zaɓen MKO inda bayan da aka soke zaɓen 12 ga watan Yuni da mai gidanta ya lashe, ta tashi tsaye wajen ganin an yi adalci.
Ya ƙara da cewa ƴan Najeriya ba za su mance da Doyin Abiola ba saboda ƙwarewarta a fannin jarida da kuma yadda take jagorantar tallafawa mata da kuma ƙoƙarin bayar da gudunmuwa a fannin dimokraɗiya.