fidelitybank

Tinubu ya mika alhininsa kan rasuwar Manjo mace soja ta farko a Najeriya

Date:

Shugaba Bola Tinubu ya bayyana mutuwar Aderonke Kale, mace ta farko da ta fara kai wa mukamin Manjo Janar a rundunar sojin Najeriya, a matsayin asara mai zafi ga kasar.

Kale, wadda kuma ita ce mace da ta fara zama kwamandar rundunar sojoji likitoci, ta rasu ne ranar Alhamis tana da shekara 84.

A cikin wata sanarwa da fadar shugaban Najeriya ta fitar, Bola Tinubu ya mika sakon ta’aziyya ga ‘ya’ya da dangin Janar Kale mai ritaya da kuma rundunar sojin Najeriya da kungiyoyin likitoci na Najeriya kan rasuwar daya daga cikinsu.

Tinubu ya ce a matsayinta na mace ta farko a fagen da ta yi zarra, marigayiyar Manjo Janar din ”mai dumbin kwarin gwiwa da kwarewar aiki da kwazo da juriya irinta matan Najeriya”.

Shugaba Tinubu ya yi addu’ar neman jin kai ga marigayiyar, kuma ya yi fatan ‘yan’uwa da dangi za su yi hakuri kan wannan rashi da suka yi.

punch newspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp