Rahotanni daga Jihar Kogi a tsakiyar Najeriya na cewa Sarkin Ibira Dr. Abdul-Rahman Ado Ibrahim ya rasu yana da shekara 95.
Kafofin yaɗa labarai na ƙasar sun ambato majiyoyi daga fadar Mai Martaba Ohinoyi na Ƙasar Ibira na cewa sarkin ya rasu ne a ranar Asabar yayin da yake jinya a wani asibiti a Abuja.
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya miƙa ta’aziyya ga iyalansa da kuma al’ummar jihar Kogi, yana mai bayyana sarkin da “ƙwararre wajen tafiyar da al’amura”. Ya yi Allah ya ji ƙan sa.
Marigayin ya hau kujerar mulki a shekarar 1997 bayan wanda ya gada, Sanni Omolorim, ya bar kujerar.
An haife shi ne ranar 7 ga watan Fabrairun 1929 kuma ya bar ‘ya’ya da jikoki da dama.