Musayar kalamai ta ɓarke tsakanin fadar shugaban, Bola Ahmed Tinubu da tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP kuma tsohon gwamanan Kano, Sanata Rabi’u Musa kwankwaso kan zargin da Kwankwason ya yi na cewar gwamantin Bola Ahmed Tinubu na ƙoƙarin ƙaƙaba dokar ta ɓaci a jihar Kano.
Yayin wani taron ƙaddamar da aiki da gwamnatin jihar Kano ta gudanar, an jiyo Kwankwaso na zargin cewa “wasu sun haɗa baki da jagororin jam’iyyar APC suna ƙoƙarin fakewa da batun rikicin masarautar Kano su tayar da fitina, don gwamnatin tarayya ta samu damar ƙaƙaba dokar ta ɓaci”.
Sai dai Fadar shugaban ƙasar ta yi watsi da zargin da Kwankwason ya yi, tana bayyana shi a matsayin marar tushe ballantana makama.
“Abun mamaki ne a ce mutum kamarsa ya fito ya yi irin waɗannan kalamai, musamman zargin da ya yi na cewar ana son a saka dokar ta ɓaci a Kano ko tayar da rikici a jihar, ko kaɗan babu ƙanshin gaskiya kan waɗannan zarge-zarge, kuma a matsayinmu na gwamnatin tarayya ba a taɓa yin makamanciyar wannan maganar ba”. Inji Abdul Aziz Abdul’aziz
Har Ila yau ya ƙara da cewa batun masarautar Kano al’amari ne da ke gaban kotu, kuma jami’an tsaro suna bin duk wani umarnin kotu don tsare hakkin kowanne ɓangare, inda ya ƙara da cewa shugaba Tinubu na da kusancin da dukkannin mutum biyun da ake taƙaddama a kansu.
“Shugaban ƙasa na da alaƙa me kyau da waɗannan mutane biyu da ake taƙaddama a kansu, ba zai yi wani abu da zai kawo cin zarafi ko ace a matsayinsa na shugaban ƙasa, da yake da alhakin kula da kare dukiya da rayukan ƴan Najeriya a ce gwamnatinsa ta yi wani abu irin wanda Rabi’u Kwankwason ya yi zargi ba, don haka mu a ganinmu ya yi kalaman ne don kawai a harzuƙa magoya baya kuma a yi siyasa” inji Abdulaziz