A ranar Larabar ne Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), ya shaidawa abokin hamayyarsa, Peter Obi na jam’iyyar Labour cewa karkatar da bayanai ba zai sa ya ci zabe ba.
Politics Nigeria ta ruwaito cewa, kalaman Tinubu na zuwa ne bayan shugaban kasar Ghana, Nana Akufo-Addo, ya musanta rubutawa Tinubu wasika, inda ya bukaci tsohon gwamnan jihar Legas da ya ba Obi dama a zaben shugaban kasa na 2023 mai zuwa.
Tinubu a cikin wata sanarwa da Bayo Onanuga, Daraktan yada labarai da sadarwa na kungiyar yakin neman zaben sa, Bayo Onanuga ya fitar, ya kuma shawarci dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour da su samu magoya bayansa da su daina yada karairayi da cin mutuncin wasu ‘yan takara musamman Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Ya danganta asalin maganganun da ake dangantawa da Shugaba Akufo-Addo ga magoya bayan Obi.


