fidelitybank

Tinubu ya mayar da martani kan mayar da Najeriya tsarin jam’iyya daya

Date:

Shugaban kasa, Bola Tinubu ya mayar da martani game da zargin da ƴan adawar ƙasar ke wa jam’iyya mai mulki na cewa tana son mayar da ƙasar kan tsarin jam’iyya ɗaya.

Tinubu ya mayar da martanin ne a cikin jawabinsa na ranar dimokurɗiyyar ƙasar, yau Alhamis 12 ga watan Yunin 2025 a zauren majalisar dokokin ƙasar.

Ya ce: “Tsarin jam’iyya ɗaya ba ya cikin manufofinmu. Kuma ba zai taɓa zama cikin manufofinmu ba.”

Sai dai shugaban ya ce wannan ba zai hana jam’iyyar APC yin maraba da duk wanda ke son shiga cikinta ba.

“Zai kasance mun yi maguɗin siyasa idan muka hana mutane daga wasu jam’iyyun siyasa shigowa jam’iyyar APC,” in ji Tinubu.

A baya-bayan nan jam’iyyar APC ta karɓi wasu daga cikin gwamnoni da sanatoci da kuma ƴan majalisar dokokin tarayya da suka sauya sheƙa zuwa cikinta daga jam’iyyun adawa.

Sai dai jam’iyyun adawar sun zargi APC da kuma shugaba Tinubu da shafa wa ƴan siyasar zuma a baki domin jan hankalinsu su koma cikin jam’iyyar mai mulki.

Tuni dai fagen siyasa na Najeriya ya ɗauki zafi duk kuwa da cewa a watan da ya gabata ne gwamnati mai ci ta ci rabin wa’adin shugabancinta na shekara huɗu.

A shekarar 2027 ne za a yi babban zaɓen ƙasar na gaba, inda ake sa ran Tinubu – wanda jam’iyyarsa ta APC ta ce shi ne “ɗan takararta ɗaya tilo” na shugaban ƙasa zai sake tsayawa takara.

Masu sharhi na ganin cewa mayar da hankali kan zaɓen na 2027 tun yanzu ba abu ne mai alfanu ga ƙasar ba, kasancewar shugabanni za su mayar da hankali kan siyasa a maimakon yin ayyukan ci gaban al’umma.

naija news legit

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp