Kungiyar Kare Hakkokin Tattalin Arziki, SERAP, ta bayar da wa’adin kwanaki 14 ga shugaban kasa Bola Tinubu kan cire tallafin man fetur.
SERAP ta ce ya kamata Tinubu ya wallafa bayanan da aka kashe na tallafin man fetur nan da makonni hudu masu zuwa.
Kungiyar ta sha alwashin fara shari’a kan Tinubu idan ya kasa wallafa bayanan nan da makonni hudu.
SERAP ta rubuta: “Cire tallafin: Mun bukaci Shugaba Tinubu ya wallafa bayanan kashe kudade na Naira biliyan 400 da aka ceto cikin makonni hudu daga cire tallafin man fetur, ko kuma mu ɗauki mataki .”
Tinubu ya bayyana kawo karshen tsarin tallafin man fetur a lokacin rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayu.
Ya sha alwashin tabbatar da cewa an karkatar da kudaden da ake kashewa wajen tallafin man fetur ga kayayyakin more rayuwa a fannonin ilimi, lafiya da sauransu.