Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC), ta ce, jam’iyyar APC ce ta lashe sakamakon zaɓen shugaban ƙasa a jihar Kwara.
Babban jami’in tattara sakamakon zaɓen shugaban ƙasa a jihar ne ya sanar da hakan a cibiyar tattara sakamakon da ke Ilori.
Ga kuri’un da manyan jam’iyyu hudu suka samu:
APC – 263,572
LP – 31,166
PDP – 136,909
NNPP – 3,141