A ranar Lahadi ne shugaba Bola Tinubu, ya bar Legas inda ya tafi zuwa Abuja nayan hutun Sallah.
Tun kafin ya tashi daga bangaren shugaban kasa na filin tashi da saukar jiragen sama na Murtala Muhammed, Tinubu a tare da Gwamna Babajide Sanwo-Olu sun yi faretin jinjina ga sojojin Najeriya.
A zamansa na kwanaki biyar a Legas, shugaban ya kai ziyarar ban girma ga manyan sarakunan Ijebu, Egba, da Eko.
Yayin zaman sa a Legas Tinubu ya karbi bakwancin shugaban kasar Guinea Bissau da shugaban hukumar ECOWAS Umaro Sissoco Embalo a gidansa da ke Legas ranar Asabar.