Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, ya ce ba Najeriya ce kadai ke fuskantar kalubale ba.
Tinubu ya bayyana haka ne da safiyar Asabar bayan kada kuri’a a mazaɓa mai lamba 085 Alausa, Ikeja.
“Ba mu kadai ne ke fuskantar matsalar tattalin arziki ba; yana yaduwa a duk duniya.
“Dole ne mu sake daidaita tsarin kuma mu sanya Najeriya a kan hanyar farfadowa,” kamar yadda ya shaida wa manema labarai.
Tsohon gwamnan na Legas ya kasance a sashin tare da matarsa, Remi Tinubu, da diyarsa Folashade Tinubu-Ojo.