Shugaba Bola Tinubu ya karbi wasikun jakadu daga kasashen Masar, Girka da Pakistan da aka aika zuwa kasar nan.
Tarbar ya baiwa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, damar sake tabbatar da dabarun da Najeriya ke da shi a Afirka, a matsayin tushen zaman lafiya, yana mai cewa al’ummar kasar nan za ta ci gaba da taka rawa a matsayin mai tabbatar da zaman lafiya a nahiyar.
Da farko da yake karbar takardar amincewa daga jakadan Masar a Najeriya, Mohamed Ahmed, ya ce, Tinubu ya jaddada aniyar kasashen biyu na inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya ta hanyar hadin gwiwa tsakanin kungiyoyin kasa da kasa, kamar Majalisar Dinkin Duniya.
Ya kuma bayyana cewa, tun bayan kulla huldar diflomasiyya a shekarar 1961, Najeriya da Masar sun hada kai kan muhimman abubuwan da kasashen duniya suka sa gaba, ciki har da samar da zaman lafiya da tsaro da kwanciyar hankali a yankin.
Tattaunawar da aka yi a taron ta kuma tabo halin da ake ciki a yankin Sahel da Sudan.
Da yake amincewa da rawar da Masar ke takawa wajen sasanta rikicin Gaza, Tinubu ya ce, A na bukatar samun zaman lafiya a yankin Gaza.
Ambasada Ahmed ya isar da aniyar shugaba Abdel Fattah el-Sisi na karfafa dangantakar tattalin arziki da Najeriya, yana mai jaddada aniyar kasar Masar na kara kasuwanci da zuba jari a tsakanin kasashen biyu.