Dan takarar shugabancin ƙasa a jam’iyyar APC, Bola Tinubu, ya kai wa Mataimakin Shugaban ƙasa Yemi Osinbajo, ziyara a fadar shugaban kasa da ke Abuja a daren Alhamis.
Bayan tattaunawa da Osinbajo, ya kuma ziyarci shugaba Muhammadu Buhari.
Tinubu ya samu kuri’u 1,271 a zaben fitar da gwanin APC, inda ya doke sauran ‘yan takara ciki har da Osinbajo wanda ya samu kuri’u 235.
Ziyarar Tinubu na zuwa ne bayan Osinbajo ya mika sakon taya murna ga Tinubu da nuna mubaya’ar aiki tare da shi, domin nasara a babban zabe.