Shugaban kasa Bola Tinubu ya kaddamar da motocin bas na farko masu aiki da Gas, CNG a fadar shugaban kasa, Abuja.
Motocin dai sun kai 20 a rukunin farko, kamfanin Innoson Motors ne ya kera su.
Gwamnati ta ce tana da kwarin gwiwar cewa motocin bas din za su taimaka wajen saukaka matsalolin sufuri musamman a babban birnin tarayya Abuja.
Biyar daga cikin motocin bas din CNG, an koro su ne zuwa bakin kofar fadar shugaban kasa, inda shugaban ya huta daga majalisar zartaswa ta tarayya, FEC, inda ya kaddamar da su.
Samar da motocin bas din na CNG na daga cikin bukatun da kungiyoyin kwadago suka yi biyo bayan cire tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ta yi a ranar 29 ga Mayu, 2023.
Ku tuna cewa Shugaban Kamfanin Innoson Motors, Cif Innocent Chukwuma, ya gana da Tinubu a makon da ya gabata a Fadar Shugaban Kasa.