Fadar shugaban ƙasa ta kaddamar da sabon jirgin shugaba Bola Tinubu.
Tinubu ya yi amfani da sabon jirgin wajen balaguro da ya yi zuwa ƙasar Faransa a ranar Litinin.
Wata sanarwa da mai bai wa shugaban shawara kan harkokin yaɗa labaru, Bayo Onanuga ya fitar, ta ce jirgin ƙirar Airbus A330 ya maye gurbin tsohon jirgin shugaban ƙasa ƙirar Boeing B737-700.
Duk da cewa sanarwar ba ta bayyana kuɗin da aka sayi jirgin ba, amma ta ce an saye shi ne da rahusa.
Onanuga ya ce sabon jirgin zai rage wa Najeriya makudan kuɗaɗe da take kashewa wajen kula da jiragen shugaban ƙasa da kuma kuɗin man wanda ya kai miliyoyin dala a kowane shekara.
Tun da farko, kwamitin kula da harkokin tsaro da kuma bayanan sirri na majalisar dattawa ne ya bayar da shawarar sauya tsohon jirgin shugaban ƙasar domin rage kuɗaɗen da ake amfani da su wajen kula da shi.

Asalin hoton,Bayo Onanuga
