Shugaban kasa, Bola Tinubu, ya bai wa ƴan wasan tawagar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta ƙasar 24 – Super Falcons – tukwicin kuɗi dala 100,000 kowanne, kimanin naira miliyan 153.
Haka nan ya bai wa kowa daga cikinsu kyautar gida mai ɗaki uku, yayin da ya bai wa tawagar masu horas da su kyautar dala 50,000.
Tinubu ya sanar da hakan ne a yau Litinin sa’ilin da ya tarbi tawagar matan bayan nasarar da suka samu ta lashe kofin ƙwallon ƙafa na Afirka karo na 10.
A ranar Asabar ne Super Falcons suka lallasa Atlas Lionesses na Morocco da ci uku da biyu a wasan ƙarshe na gasar cin kofin da Moroccon ta karbi baƙunci.
Baya ga kyautar kuɗi da gida, Tinubu ya kuma karrama ƴan wasan da lambar girmamawa ta ƙasa ta OON.
Haka nan kuma ƙungiyar gwamnonin Najeriya ta bai wa tawagar ta Super Falcons kyautar kudi naira miliyan 10.
A lokacin da yake jawabi, Tinubu ya ce: “Na karɓi wannan kofi a madadin ƴan Najeriya, kuma zan ce muku: mun gode da wannan ƙwazo, saboda haka na karrama ƴan wasan da masu horas da su 11 da lamabar girmamawa ta Officer of the Order of the Niger (OON).
“Bugu da ƙari na bayar da umarnin a bai wa dukkanin ƴan wasa da masu horas da su gidaje masu ɗakuna uku-uku.
“Haka nan kuma, akwai kyautar kudin naira kwatankwacin dala 100,000 ga kowace ƴar wasa 24 da kuma dala 50,000 ga tawagar masu horaswa.”