Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya halarci sallar Idin ne a filin Idi na ‘Dodan Barak’ da ke unguwar Obalende a birnin Legas.
Bayan kammala sallar, Tinubu ya buƙaci al’ummar Najeriya su guji rikice-rikice na banbancin addini da na ƙabila.
Waɗanda suka raka shugaban ƙasar wurin sallar sun haɗa da mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu, da shugaban ma’aikatan fadar gwamnati, Femi Gbajabiamila, da kuma toshon ministan ayyuka da gidaje Babatunde Raji Fashola.