fidelitybank

Tinubu ya gargaɗi ɗansa da kakkausar murya kan shiga sherri ba shanu

Date:

Shugaba Bola Tinubu a ranar Litinin, ya gargadi dansa, Seyi, da sauran mutane da su kaurace wa halartar ba taron majalisar zartarwa ta tarayya (FEC).

Tinubu ya bayyana karara cewa wadanda aka amince da su ne kawai ake ba su damar zama a taron majalisar ministocin na mako-mako.

“A makon da ya gabata, na lura da yadda mutane ke shiga da fita daga wannan majalisa ba bisa ka’ida ba.

“Na ga hoton ɗana, Seyi, zaune a baya. Wannan ba abin yarda ba ne.

“Zan sanar da ku mutanen da ya kamata su kasance a nan,” in ji shi.

Shugaba Tinubu ya ci gaba da bayyana sunayen masu ba shi shawara na musamman kan harkokin siyasa, Hadiza Usman; Bayani da Dabaru, Bayo Onanuga; Babban Sakatare mai zaman kansa, Hakeem Muri-Okunola da Sakatare mai zaman kansa, Damilotun Aderemi.

“Waɗannan su ne mutanen da aka keɓe don kasancewa a nan lokacin da muke gudanar da kasuwancin ƙasar. Sai dai in na aika a kira ku, kar ku zo, ku bayyana a sarari,” in ji Tinubu.

vanguard 
nigeria

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Kare Ya Kashe Ragon Layya: Mai ƙwacen waya ya kashe Sojin ruwa a Kaduna

Wani mai ƙwacen waya ya kashe wani soja bayan...

Sojoji sun hallaka ƴan Boko Haram da dama

Da sanyin safiyar ranar Litinin, dakarun rundunar Haɗin kai...

Tarzomar kama baƙin haure a Amurka na yamutsa hazo

An shiga rana ta uku a tarzomar da ake...

Alhazai sun kammala aikin Hajji bana

A ranar Lahadin da ta gabata ne alhazai miliyan...

Tinubu gyaran ƙasa za ka mayar da kai ba zaɓen 2027 ba – ACF

Ƙungiyar Tuntuɓar Juna ta Arewacin Najeriya, ta yi kira...

Ƴan Jagaliya sun caka wa Matashi kuwa lokacin da ya zo karɓar naman Sallah a Kano

Matashi Ibrahim Mahmud ya rasu sakamakon caka masa wuƙa...

Kallo Ya Koma Sama: Elon Musk zai fuskanci mummunar sakamako – Trump

Ana ci gaba da takun saka tsakanin shugaban Amurka...

Zulum ya miƙa kyautar Naira miliyan 100 ga iyalan Sojojin da aka kashe

Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno, ya bai...

Otal ɗin ƴan Najeriya ya kama da wuta wani ɓangaren a Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce an samu tashin...

An kai hari maɓoyar Boko Haram a Borno

Biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu, rundunar...

Alaƙar Trump da Elon Musk ta yi tsami sosai

Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon...

An yi jana’izar Muhammad Uwais

An gudanar da jana'izar tsohon alkalin alkalan Najeriya, mai...
X whatsapp