Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya umurci kamfanonin siminti a Najeriya da su koma kan tsohon farashin kayayyaki a lokacin da ake kara tsadar kayayyaki.
David Umahi, ministan ayyuka ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis bayan ya duba kamfanin siminti na BUA a jihar Sokoto.
Umahi ya ce, “Shugaban kasa ya dage da cewa su koma yadda suke a halin da ake ciki dangane da wannan farashin siminti na talaka.
“Ina so in ba su kwarin guiwa da su bi umarnin shugaban kasa domin mu cimma gagarumin shirin samar da gidaje da kuma sabon tsarin bege na sabbin hanyoyi na shugaban kasa,” in ji shi.
Buhunan siminti sun kai N10,000 da 15,000 a Abuja daga N5,000.
A wajen siminti kuma, farashin sauran kayayyakin gini ya yi tashin gwauron zabi.
A watan da ya gabata ne gwamnatin Najeriya ta bakin ministan gidaje da raya birane Ahmed Dangiwa, ta yi barazanar bude kan iyakokin kasar domin shigo da siminti idan masana’antun suka gaza rage farashin kayayyaki.